Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

Image
 8th March, 2025  Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar …As Forum Crowns Gombe Governor ‘Khadimul Qur’an’ …Lauds Him for Construction of Tsangaya Schools, Free Enrollment of Almajiri into Go-Health Governor Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, has hosted the leadership of the Association of Tsangaya teachers from across the state to a special Iftar at the Government House, Gombe.  This was a continuation of the Governor’s tradition of hosting public Iftar for the citizens of the state, an occasion that provides Governor Inuwa Yahaya with another opportunity to deepen his engagement with the Muslim community and promote peace and brotherhood among all. Addressing his guests shortly after the iftar, Governor Inuwa Yahaya reaffirmed his administration’s commitment to improving the welfare of Tsangaya teachers and Almajiri children, acknowledging the significance of Qur’anic education in the society. The Governor stated that his government has ensured the provision o...

Jihar Gombe Ta Shirya Taron Tsaro Na Karo na Biyu, Yayin da Gwamna Inuwa Yahaya Ya Ba Da Gudunmawar Motoci 50 Ga Hukumomin Tsaro

 26 Ga Watan Fabreru, 2025

Jihar Gombe Ta Shirya Taron Tsaro Na Karo na Biyu, Yayin da Gwamna Inuwa Yahaya Ya Ba Da Gudunmawar Motoci 50 Ga Hukumomin Tsaro


…“Gombe Na Daya Daga Cikin Jihohin da Suka Fi Zaman Lafiya a Najeriya” – Kwamandan Rundunar Sojoji ta 3, Manjo Janar Oyinlola




Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya bude taron tsaro na kwanaki biyu karo na biyu wanda ake gudanarwa a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa (ICC) a Gombe.


Taron, mai taken “Gina Gombe Mai Tsaro da Lumana: Magance Matsalolin Tsaro Ta Hanyar Hadin Gwiwa”, an shirya shi ne domin tattaro masu ruwa da tsaki don tattaunawa, gano matsaloli, da tsara hanyoyin magance kalubalen tsaro da ke addabar jihar da yankin Arewa maso Gabas gaba daya.


A jawabin sa, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da shawarwarin da aka cimma a taron don tsara wata manufa mai dorewa wacce za ta taimaka wajen magance dalilan da ke haddasa rikice-rikice da rashin tsaro a jihar.


Gwamnan ya jaddada cewa samar da tsaro shi ne babban nauyin kowace gwamnati, domin ba za a samu zaman lafiya ba idan babu tsaro. Ya kara da cewa gwamnatinsa na ba da fifiko ga tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.


Ya bayyana cewa duk da zaman lafiyar da ake morewa a Gombe, jihar na fuskantar wasu matsaloli kamar rikicin manoma da makiyaya, rikice-rikicen kabilanci, da sauransu. Saboda haka, yana da matukar muhimmanci a hada kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin magance wadannan matsaloli gaba daya.


“Ko da yake Gombe tana cikin jihohin da ke da kwanciyar hankali, tana fama da wasu matsaloli da suka hada da tasirin rikice-rikicen da ke faruwa a makwabtan jihohi, rikice-rikicen tarihi irin na manoma da makiyaya, da kuma barazanar sabbin laifuka kamar satar shanu, 'yan fashi, garkuwa da mutane, da sauran manyan laifuka.


Domin magance wadannan matsaloli gaba daya, dole ne mu rungumi hadin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki: hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, kungiyoyin farar hula, kafafen yada labarai, da masu zaman kansu,” in ji shi.


Gwamnan ya kara da cewa wajibi ne a magance tushen matsalolin rashin tsaro, yana mai jaddada bukatar samar da hanyoyin da za su hana matasa fadawa cikin ayyukan laifi.


“Dole ne mu tashi tsaye wajen yaki da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi tsakanin matasanmu. Haka kuma, dole ne mu yi kokari wajen bunkasa basirarsu ta hanyar samar da ilimi, horo, da damammakin da za su taimaka musu su yi nasara a wannan zamani da ke cike da sauye-sauye.”


Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan ci gaban da ake samu wajen yaki da 'yan ta’adda, 'yan fashi, da sauran laifuka a kasar.


“Ina mika godiya ga Shugaban Kasa bisa kokarinsa na tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali, da kuma kare martabar Najeriya.


Haka kuma, muna matukar godiya ga Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da tsaron Najeriya.”



Gwamnan ya kuma sanar da bayar da gudunmawar motoci 50 ga hukumomin tsaro domin su samu damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.


“A matsayin wani bangare na kokarinmu na kara inganta tsaro a Jihar Gombe, ina mai farin cikin sanar da bayar da gudunmawar motoci 50 ga hukumomin tsaro daban-daban da ke aiki a jihar.


Wannan gudunmawa na da nufin kara karfafa aikin hukumomin tsaro wajen yaki da aikata laifuka, tabbatar da zaman lafiya, da kiyaye tsaro a al’ummominmu.”


A cikin jawabin da ya gabatar, Kwamandan Rundunar 3 ta Sojojin Najeriya, kuma Kwamandan Rundunar Operation Safe Haven, Manjo Janar Folusho Oyinlola, ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya kan fifiko da yake bai wa sha’anin tsaro, yana mai bayyana cewa hakan yana da matukar muhimmanci ga ci gaban kowace al’umma.



Ya ce Gombe tana daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya, yana mai cewa hakan ba kawai sakamakon sa'a ba ne, illa sakamakon ingantattun manufofin da gwamnatinsa ke aiwatarwa wadanda ke ba da damar hadin gwiwar masu ruwa da tsaki wajen kare rayuka da dukiyoyi.


A yayin taron, an gabatar da jawabai daga manyan masana tsaro da suka hada da: Janar Abdulrasheed Aliyu (mai ritaya), wanda ya gabatar da maqala mai taken “Muhimmancin Fasaha da Bincike a Yaki da Matsalolin Tsaro”, AIG Zubairu Mu’azu (mai ritaya), wanda ya gabatar tasa qasidar kan “Muhimmancin 'Yan Sanda na Al’umma Wajen Kara Inganta Tsaro a Matakin Kasa: Nazarin Yankin Arewa”


Ana sa ran mahalarta taron za su sami ilimin da zai ba su damar tsara dabarun da suka dace domin inganta tsaro a Gombe, Arewa maso Gabas, da Najeriya gaba daya.

A farkon taron, Kwamishinan Harkokin Tsaro da Al’amuran Cikin Gida, Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya), ya bayyana cewa wannan taron tsaro na biyu yana daga cikin muhimman matakan da gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ke dauka domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a jihar.

An dai kaddamar da sabbin motocin sintiri guda 50 da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayar tare da mika makullansu ga hukumomin tsaro da suka ci gajiyar su.

Daga:

Ismaila Uba Misilli

Daraktan Yada Labarai,

Gidan Gwamnati, Gombe.

dailygombe.blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

Gombe SSG Prof Njodi celebrates Yazu's recognition by GSU

Ag. VC na Jami'ar Jihar Gombe GSU, ya jinjina wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ba da fifiko ga ilimi.

AWARD: Njodi, Kallamu, Adamu,Umar Bags National leadership Award of Excellence.