Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

17/11/2024
Gwamnan Gombe Ya Taya Aiyedatiwa Da APC Murnar Nasarar Lashe Kujerar Gwamnan Ondo
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya taya takwaransa na Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa na Jam'iyyar APC murnar samun gagarumin rinjaye a zaɓen gwamnan Jihar Ondo da aka kammala, wanda ya ƙara tabbatar da aniyarsa ta jan ragamar jihar a wani sabon wa'adi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana nasarar da Aiyedatiwa ya samu a matsayin nasarar da ta tabbatar da aminci da amanar da al’ummar Ondo suke da shi a ga jagorancinsa.
Yace babbar tazarar data baiwa gwamnan nasara ta nuna ƙarara irin goyon bayan tsarin tafiyar da mulki na Jam’iyyar APC da kuma shugabancinta na ƙasa ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke ci gaba da jan hankalin al’ummar Nijeriya.
A yayin da ya bukace shi da ya ci gaba da bin ka’idojin jam’iyyar na samar da ayyuka da shugabanci na gari, Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma buƙaci gwamnan da aka sake zaɓa ya ci gaba da baiwa al’ummar Ondo fifiko da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa da za su yi kyakkyawan tasiri a rayuwarsu.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa Aiyedatiwa da gwamnatinsa jagora, ya ba shi hikimar ci gaba da ayyukan alherin da ya fara.
Daga:
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment