Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

13/11/2024
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya Ga Iyalan Marigayi Shahararren Malamin Al-Qur'ani, Goni Sani.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Goni Muhammad Sani, fitaccen malamin Alƙur’ani, wanda ya rasu bayan fama da jinya.
Gwamnan ya ziyarci gidan marigayin dake Unguwar Yelenguruza a cikin birnin Gombe don jajantawa iyalan marigayin da ɗimbin ɗaliban da ya bari.
A yayin ziyarar, Gwamna Inuwa Yahaya ya jajanta musu, inda ya buƙaci su rungumi ƙaddara su kuma yi haƙuri duba da irin kyawawan ayyuka da ɗabi'un da marigayi malamin ya bari.
Yace marigayi Goni Muhammad Sani ya yi fice a wa'azozi da karantar da Alkur’ani, inda ya yaba da jajircewar da ya yi a tsawon rayuwarsa kan koyar da 'ilimin addinin Musulunci.
Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Goni Murtala Chashiya, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya da gwamnatinsa bisa goyon bayan da suka bayar da kuma taya iyalan alhini a lokacin da suke cikin jimami.
An yi addu'o'i na musamman na neman Allah Madaukakin Sarki ya jiƙan marigayin Malamin ya saka masa da gidan Jannatul Firdausi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnati da suka hada da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi; da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Abubakar Inuwa Kari; da kwamishinoni, da sauran manyan jami'ai.
Daga:
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment