Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

LABARI ACIKIN HOTO:
Shugaban ƙaramar hukumar Gombe ya ziyarci Babbar kasuwar Gombe domin ƙira ga yan kasuwa da su sauƙaƙawa talakawa tunda sunfara saro kayan masarufi mai da araha.
Maigirma shugaban ƙaramar hukumar Gombe kuma shugaban ALGON Barr. Sani Ahmad ya jagoranci tawaga mai ƙarfi suna shiga lungu da sako na Babbar kasuwar Gombe suna ƙira ga yan kasuwa da su tausayawa talakawa suna rage farashi matuƙar sun sayi kayan da sauƙi.
Kana shugaban ya gargadi masu amfani da mudu tauyayye wajen awu da suji tsoron Allah hakan na iya zaman towa masifa wa gari baki daya sannan kuma a ƙwace wannan kwanon awun domin kada abarsu su cigaba da amfani dashi.
Daga cikin tawagar ya haɗa da Babban kwamandan civil Defence M.B Mu'azu da kuma shugaba kasuwar ƙauye Alh. Uba Abdullahi da dai sauransu.
Daga Sufee Gombe
Comments
Post a Comment