Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

LABARI ACIKIN HOTO:
Shugaban ƙaramar hukumar Gombe Barr Sani Ahmad Haruna ya gana da jami'an tsaro da shuwagabannin kungiyoyi da Matasa domin gujewa fitinar zanga zanga.
Maigirma shugaban ƙaramar hukumar Gombe kuma shugaban ALGON, Barr. Sani Ahmad yayi zama da jami'an tsaro na ƴan sanda da civil defence da shuwagabannin kungiyoyin yan kasuwa da kuma matasa a babban dakin takin taro dake ma'aikatar ƙaramar hukumar Gombe.
A yayin zaman, Babban kwamandan na civil defence na jihar Gombe M.B Mu'azu yaja hankalin shuwagabannin kungiyoyi da matasa da su guji harkar Zanga Zanga don bata taba haifar da alheri ba, haka zalika suma DPO na caji ofis din Gombe da na caji ofis din low-cost sunyi kira ga matasa da su guji wannan harka ta Zanga zanga.
Suma shuwagabannin ƙungiyoyin sun tabbatar da cewa sun gargadi mambobinsu daga shiga sabgar Zanga zanga kuma baza a taba samun wani daga cikin mambansu da zai shiga sabgar Zanga zanga ba, Haka zalika matasa suma sunce basu ba zanga zanga domin in kasan farkon fitina bakasan ƙarshen ta ba.
Daga karshe shugaba ya kuma rufe da jawabin inshaallah za'a baiwa mata da matasa tallafi kuma za'a baiwa mutum 400 a kowace gunduma.
Comments
Post a Comment