Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

28/06/2024
Gwamnatin Gombe Ta Dakatar Da Dagaci Da Kansila Bisa Zarginsu Da Satar Transfomer
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da dakatar da Dagacin Garin Majidadi dake Ƙaramar Hukumar Akko, Mohammed Majidaɗi nan take.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a.
Hakazalika, Majalisar Karamar Hukumar Akko, bisa dogaro da dokar Kananan Hukumomi ta Jihar Gombe ta 2013, ta sanar da dakatar da Kansila mai wakiltar Kumo Gabas, Abdullahi M. Panda.
Dakatarwar ta biyo bayan badaƙalar data shafi jami’an biyu ne, waɗanda rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta kama, kuma a halin yanzu suke fuskantar shari’a kan zargin haɗin baki wajen sata da kuma sayar da randar wutar lantarkin wato transfoma na Garin Majidaɗi.
Dakatar da jami'an biyu wani mataki ne na tabbatar da cewa ba a samu karan tsaye wa harkokin shari'a ba.
Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya jaddada ƙudurinsa na tabbatar da bin doka da oda a kodayaushe, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa adalci zai tabbata, kuma doka za ta yi aikinta, ba kawai a kan Majidaɗi da Panda ba, har ma da duk wassu mutanen da aka samu da hannu a satar.
Daga:
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
English Translation
28th June, 2024
Gombe Government Suspends Village Head, Councillor Over Alleged Involvement in Transformer Theft
Gombe State Governor, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, has approved the immediate suspension of the Village Head of Garin Majidadi in Akko Local Government Area, Mohammed Majidadi.
The Secretary to the State Government, Professor Ibrahim Abubakar Njodi announced the decision in a statement released today.
Similarly, the Akko Local Government Council, relying on the authority of the Gombe State Local Government (Amendment) Law, 2013, also announced the suspension of the Councillor representing Kumo East Ward, Abdullahi M. Panda.
The suspensions come in the wake of recent developments involving the two officials, who were paraded by the Gombe State police command, and currently facing trial over allegations of conspiracy in the theft and subsequent sale of a community electricity transformer at Garin Majidadi.
The suspension of both officials is a preventive measure to ensure that there is no interference in the legal process.
Governor Inuwa Yahaya, who stressed commitment to always upholding the rule of law, expressed his confidence that justice will prevail and that the law will take its course, not only against Majidadi and Panda but also against any other individuals found to be complicit in the theft.
From:
Ismaila Uba Misilli
Director-General
( Press Affairs)
Gombe
Comments
Post a Comment