Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

29/06/2024
Gwamnan Gombe Ya Yi Zama Da Majalisar Dottawa Masu Bashi Shawara
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya yi taron rubu'i-rubu'i jiya Juma'a da dottawa 'yan majalisan bashi shawara na Jihar Gombe a masauƙin Gwamnan dake Abuja.
Majalisar wacce ke ƙarƙashin jagorancin Emeritus Farfesa Idris Mohammed ta ƙunshi fitattun masana daga ɓangarori daban-daban, inda ta tattauna batutuwa da dama da suka shafi jihar.
Muhimman batutuwan da aka tattaunan sun haɗa da ƙoƙarin inganta zuba jari, da haɓaka ilimi mai zurfi, da sauye-sauyen fansho, da kula da ma'aikatan kiwon lafiya, da sabbin dabarun yaki da ƙalubalen yaran da ba sa zuwa makaranta.
Majalisar ta kuma samar da ingantattun hanyoyin magance wassu muhimman batutuwan raya ƙasa kamar samar da makamashi, da bunƙasa noma, da kuma matakan da ake ɗauka na rage raɗaɗin tsadar rayuwa ga al'ummar Jihar Gombe.
A yayin taron, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada muhimmancin yin aiki tare da masu ba da shawaran don ciyar da Jihar Gombe gaba.
Yace bayanai da shawarwarin da majalisar ta bayar za su taimaka wajen tsara manufofi da aiwatar da shirye-shiryen inganta rayuwar al’ummar Jihar Gombe.
Emeritus Farfesa Idris Mohammed ya yabawa Gwamnan bisa yadda yake tafiyar da harkokin mulki da kuma ƙudurinsa na yin amfani da kwararru wajen magance ƙalubale daban-daban da Jihar Gombe ke fuskanta.
Majalisar wacce ke zama wata babbar zauren ba da shawara na jihar, Gwamna Inuwa Yahaya ne ya kafa ta a bara don taimakawa wajen tsara manufofi masu muhimmanci don ci gaban jihar da kuma gano ingantattun hanyoyin magance ƙalubalen ci gaba da jihar ke fuskanta.
Daga:
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
English Translation
29th June, 2024
Gombe Governor Holds Quarterly Meeting with Honorary Advisory Council
Governor Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, has convened a quarterly meeting with members of Gombe State Honorary Advisory Council at the Governor’s Lodge in Abuja.
The council, chaired by Emeritus Professor Idris Mohammed and composed of eminent experts from diverse sectors, discussed a broad range of critical issues affecting the state.
Key topics of discussion included investment promotion, higher education, pension reforms, human resource management in the health sector, and innovative strategies for combating the challenge of out-of-school children.
The council also identified effective solutions for several vital development issues such as energy infrastructure, agricultural development, and measures to mitigate the impact of the current cost of living crisis on the residents of Gombe State.
During the meeting, Governor Inuwa Yahaya emphasized the importance of the engagement with the honorary advisors in driving the state's development agenda forward.
He noted that the insights and recommendations from the council would be instrumental in shaping policies and implementing programmes aimed at improving the socio-economic well-being of the people of Gombe State.
Emeritus Professor Idris Mohammed commended the Governor for his inclusive governance and his resolve to leverage expertise in addressing the diverse challenges facing Gombe State.
The Advisory Council, serving as the state’s premier advisory body, was established last year by Governor Inuwa Yahaya to guide the formulation of strong policies for the state’s development and to identify effective solutions to development challenges the state faces.
From:
Ismaila Uba Misilli
Director-General
( Press Affairs)
Government House
Gombe
Comments
Post a Comment