Governor Inuwa Yahaya Hosts Tsangaya Teachers to Iftar

05/12/2023
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Yi Jimamin Rasuwar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Aliyu Usman Haruna
Muna bakin cikin sanar da rasuwar Alhaji Aliyu Usman Haruna, Shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Gombe.
Allah ya yiwa Alhaji Aliyu mai shekaru 58 rasuwa ne yau a wani asibitin ƙasar Masar inda yake jinya.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya samu labarin rasuwar Alhaji Haruna cikin tsananin bakin ciki da damuwa.
Da yake tsokaci game da wannan labari na baƙin ciki, Gwamnan ya bayyana rasuwar Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Jihar (ALGON) a matsayin babban rashi, ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma da Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.
Ya bayyana marigayin a matsayin amintaccen abokin aiki, mai gaskiya da riƙon amana, lamarinda yasa wannan rashin ya zama ya taɓa shi matuƙa.
Gwamna Inuwa yace mutuwar shugaban ƙaramar hukumar Gomben ba rashi ne ga ƙaramar hukuma ɗaya kawai ba, rashi ne ga Jihar Gombe baki ɗaya.
Yace Alhaji Haruna ɗan siyasa ne mai tawali’u da mutunci, kuma fitaccen ɗan siyasa kana shugaba wanda ya yiwa al’ummar ƙasa hidima ta ɓangarori daban-daban, wanda ya taɓa rayuwar mutane da dama.
"Halayen shugabancin Alhaji Aliyu Haruna da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al'ummarsa sun bayyana a duk tsawon aikin da ya yi a matsayin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe da kuma matsayin na riƙo da yake kai, dama sauran muƙamai da ya riƙe".
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, da al’ummar Ƙaramar Hukumar Gombe dama na ɗokacin jihar baki ɗaya.
Yace “Yayin da muke alhinin wannan babban rashi, muna addu’ar Allah Ta’ala ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da Aljannar Firdausi”.
An haifi marigayi Alhaji Aliyu Haruna wanda aka fi sani da Ali Ashaka ne a ranar 2/6/1965, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 16.
Za a sanar da lokacin jana'izarsa nan gaba kaɗan.
Daga:
Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Comments
Post a Comment